
Shafin yada labarai na Alwafd ya bayar da rahoton cewa, wasu daga Falastinu sun ziyarci masallacin Imam Hussain (AS) da e birni Alkahira na kasar Masar.
Bayan kammala ziyarar, limaman Falasdinawa sun bayyana jin dadinsu kan ziyara a wadannan wurare masu dimbin tarihi, wadanda suka sha jin ta bakin masana tarihi a kansu, tare da gode wa ma'aikatar kula da ayyukan addini ta Masar bisa aiwatar da wasu shirye-shirye na bayar da horo na hadin gwiwa a fannonin kimiyya da al'adu.
Ziyarar ta kuma samu halartar manyan jami'an ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar, da jami'an Azhar da kuma limamin masallacin Imam Hussein da ke birnin Alkahira.
Masallacin Imam Husaini (AS) an gina shi ne a birnin Alkahira a zamanin khalifancin Fatimiyyah kuma yana daya daga cikin manya-manyan masallatai mafi girma a cikin birnin.