IQNA

Kwamitin Kula Da Fursunoni Falastinawa Da Ke Hannun Isra'ila Ya Koka Kan Mawuyacin Halin Da Fursunonin Suke Ciki

20:53 - February 08, 2022
Lambar Labari: 3486925
Tehran (IQNA) Kwamitin Falastinawa da ke kula fursunonin Falastinawa da Isra'ila ke tsare da su ya koka kan mawuyacin halin da fursunonin suke ciki.

A cikin wani bayani da ya fitar a yau, Kwamitin Falastinawa da ke kula da fursunonin Falastinawa da Isra'ila ke tsare da su ya koka kan mawuyacin halin da fursunonin suke ciki.

A wani rahoton kuma kamfanin dillancin labaran Wafa na Falasdinu ya rawaito cewa sojojin Isra'ila sun kashe wasu Falastinawa uku a yau lamarin ya faru ne a unguwar al-Makhfeya da ke birnin na Nablus.

Rahoton ya kara da cewa, shafin sadarwa na yanar gizo na hukumar Falastinawa ya ce, dakarun na musamman na Isra’ila sun kai hari a unguwar ne da wata motar farar hula dauke da lambar Falasdinu.

Daga nan ne sojojin suka fara bude wuta kan wata motar da ke tafiya a kusa da wajen, inda suka kashe uku daga cikin mutanen da ke cikinta tare da kame na hudu.

Dakarun Al-Aqsa Martyrs Brigade sun bayyana wadanda abin ya shafa a matsayin mambobin kungiyar gwagwarmayar da ke Yammacin Kogin Jordan, inda ta bayyana sunayensu da Ibrahim al-Nablusi, Adham Mabrouk, da Muhammed al-Dakhil.

 

4034468

 

 

 

 

captcha