
Yayin da yake ganawa ta wayar tarho da firaministan kasar Japan Kishida Fumio, Ibrahim Raisi ya yi maraba da yadda ake samun karfafar dangantaka da ke tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa: Iran da Japan kasashe biyu ne masu matukar muhimmanci da tarihi na zaman lafiya a tsakaninsu.
Shugaban ya ce: "bisa la’akari da irin karfin da kasashen biyu ke da shi, za mu iya daukar manyan matakai don karfafa dangantakar da ke tsakanin Teheran da Tokyo."
Har ila yau Raisi ya jaddada bukatar samar da dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya inda ya ce: Tehran da Tokyo za su iya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Asia da kuma karfafa hadin gwiwa.
Haka nan kuma Shugaban ya bayyana bakin kasashen waje a cikin harkokin yankin gabas ta tsakiya a matsayin babban abin da ke haddasa rashin tsaro a yankin, tare da jaddada bukatar warware rikicin kasar Yemen ta hanyar shawarwarin ‘yan kasar a tsakaninsu.
Shi ma a nasa bangaren firaministan kasar Japan Kishida Fumio ya taya shugaba Ra’isi murnar zagayowar ranar samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran, inda ya ce: Na sha zuwa Tehran sau da dama a lokacin ina aiki a ma'aikatar harkokin wajen kasar Japan, da kuma lokacin da ina shugabancin kungiyar sada zumunci tsakanin Iran da Japan.
Kuma yanzu haka muna da burin kara haɓaka matakin alaƙa tsakanin kasashen namu, ta yadda al’ummominsu za su ci moriyar juna.