IQNA

Masani: Musulmin India Sun Zama saniyar Ware A Cikin Kasarsu

23:20 - February 13, 2022
Lambar Labari: 3486944
Tehran (IQNA) Noam Chomsky ya ce kyamar addinin Islama ta dauki salo mafi muni a Indiya.

Fitaccen masani dan kasar Amurka Noam Chomsky ya ce kyamar addinin Islama ta dauki salo mafi muni a Indiya, lamarin da ya mayar da kusan mutane miliyan 250 'yan tsiraru da ake nema ruwa a jallo.

Pakistan Observer ta sanar da cewa, a cikin wani sakon bidiyo da ya aikewa wani gidan yanar gizo da majalisar musulmin Indo-Amurka ta shirya, fitaccen mai bincike Chomsky  ya soki yadda gwamnatin Indiya ke mu'amala da musulmi, yana mai cewa yayin da cutar kyamar Musulunci ke karuwa a kasashen yammacin duniya, wannan shi ne mafi muni.

Chomsky ya kuma ce gwamnatin Narendra Modi mai ra'ayin kishin addinin Hindu, ta kara zafafa laifukan da ta ke yi a yankin Kashmir da Indiya ta mamaye.

Laifukanta a Kashmir da take aikatawa na da dadadden tarihi, inda ya kara da cewa a yanzu Kahemir ta zama yankin da aka mamaye, kuma ikon sojojinta ya yi kama da na Falasdinu da ta mamaye.

Baya ga Chomsky, masana ilimi da masu fafutuka da yawa sun shiga cikin  yanar gizo domin yaki da maganganun ƙiyayya da tashin hankali a Indiya."

4036043

 

 

captcha