
Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Abul Gaith ya jaddada cewa, ba za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsaro a yankin ba, har sai idan an kawo karshen mamayar da Isra'ila ke yi a yankunan Falasdinu.
Kamfanin dillancin labaran sputnik ya habarta cewa, Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Abul Gaith ya ce har yanzu kasashen Larabawa na cikin wani mawuyacin hali na tarihi inda barazanar siyasa ke ci gaba da yaduwa.
Ya kara da cewa: "Kalubalen tsaro, tattalin arziki da zamantakewa da al'ummominmu da gwamnatocin mu ke kara ke fuskanta yana kara ta'azzara, kuma har yanzu suna fuskantar munanan manufofi a yankin da kuma fadada manufofin wasu gwamnatoci a yankin da nufin fadada mulkin mallaka da tasiri."
Babban sakataren kungiyar hadin kan Larabawa ya ci gaba da nuna da damuwar Larabawa yana mai cewa: Dukkanmu muna da alhakin kare Falasdinu.
Ya kara da cewa: Zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki yana yiwuwa ne idan aka kawo karshen mamayar Isra'ila a Falasdinu da kuma kafa kasar Falasdinu a cikin iyakokin 1967 na birnin Kudus.
https://iqna.ir/fa/news/4037069