IQNA

Wanda ya kafa tarihi a duniya a wasan ninkaya ya zama musulmi

20:46 - March 15, 2022
Lambar Labari: 3487057
Tehran (IQNA) Mutumin da ke rike da kambun tarihi na duniya a wasan iyo ko ninkaya Vladislav Shuliko na kasar Kyrgyzstan ya musulunta.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya ketare tafkin Issyk-Kul; Kyrgyzstan Pearl ce ke rike da tarihin.

A cewar hukumar al'adu ta Iran a Kyrgyzstan, Shuliko mai shekaru 21 ya fara tseren gudun fanfalaki ne a ranar 22 ga watan Agustan shekarar 2021 da karfe 19:30 kuma ya yi tafiyar kilomita 180 daga Karakol zuwa Balikchi cikin kwanaki 6.

Isik tabki ne da ke arewacin tsaunin Tianshan a Kyrgyzstan; shi ne tafkin da ke kan  dutse mafi muhimmanci a yankin Turkestan da Kyrgyzstan kuma daya daga cikin manyan tafkunan tsaunuka mafi girma da dadi a duniya.

 

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4043035

captcha