IQNA

21:46 - March 18, 2022
Lambar Labari: 3487069
Tehran (IQNA) A yau ne aka gudanar da sallar Juma'a a masallacin Al-Aqsa tare da halartar dubun dubatar Falasdinawa, duk kuwa da tsauraran matakan da gwamnatin sahyoniya ta dauka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palestine Today cewa, dubban Falasdinawa ne suka taru a gaban masallacin Al-Aqsa inda suka gudanar da sallar Juma’a duk da tsauraran matakan da ‘yan mamaya suka dauka da kuma tsananin sanyi.

A cikin wannan wa'azin, Sheikh Mohammed Hussein, Muftin Kudus da Falasdinawa, ya yi kira ga Palasdinawa da su je masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan, da kuma taimaka wajen sake gina shi.

Tsohon birnin na Kudus ya ga dimbin ‘yan sanda da dakarun mamaye, wadanda ke tauye masu ibada da kuma hana su shiga ta hanyar bincike, kamawa, ko kuma tantance sunayensu.

Hakazalika 'yan sandan gwamnatin mamaya dauke da muggan makamai sun hana masu ibada da dama shiga masallacin Al-Aqsa da ke gabar yammacin kogin Jordan domin gudanar da sallar asuba da Juma'a.

Da safiyar yau ne dakarun gwamnatin mamaya a birnin Kudus suka kai hari kan wani matashi Bafalasdine daga gabar yammacin kogin Jordan da ke tsallaka titin Al-Wad a tsohon birnin.

Mazauna garin Jabal Makbar da ke birnin Kudus ma sun gudanar da sallar Juma'a a filin wasa na birnin don nuna adawa da manufar tsananta rusa gidajensu.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4044004

Abubuwan Da Ya Shafa: dubun-dubatar Falasdinawa ، Masallacin Al-Aqsa ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: