
Musulmai da wasu limaman masallatan Delhi sun ce kwatsam 'yan sanda sun dakatar da sallar Juma'a kuma sun ki yin bayani ko kuma bayar da wata takarda dake dauke da umarnin kotu kan hakan.
Lamarin ya fito fili ne a lokacin da Zafar al-Islam, tsohon shugaban hukumar tsiraru ta Delhi, ya raba wani hoto a jaridar Inquilab inda ya ce a ranar Juma'a 'yan sandan Delhi sun hana al'ummar musulmi yin salla a masallatai.
Ya rubuta a cikin wani sakon twitter cewa: 'Yan sanda sun hana sallar Juma'a a masallatai 16 a gundumar Punchshil dake Delhi.
Limamamin tsohon masallacin ya ce wannan shi ne karon farko da ake rufe masallattai tare da hana musulmi yin sallah a nan cikin shekaru hamsin.
Niaz Ahmad, Limamin Masallacin Lal Gonbad ya ce: "Ina zaune a nan tun a shekarun 1980, kuma na fara Iimanci wannan masallaci a shekarun 2000." Wannan bai taba faruwa a baya ba.
Ya ci gaba da cewa: Ina tsammanin sun dauki matakin ne saboda bikin Holi na Hindus, amma na gaya musu cewa halin da ake ciki a nan ba abin damuwa ba ne, shekara biyar ko fiye, Holi da Juma'a suna faɗuwa a rana ɗaya, amma duk ana yin Juma'a kuma ana bikin holi ba tare da wata matsala ba.
Mohammad Khalid limamin masallacin Naeem yana cewa: ‘Yan sanda sun zo wurinmu suka ce ba za a yi sallah a masallacin yau ba. Da aka tambaye su dalili, sai suka ce Hukumar Archaeological Directorate ta umarce su da su hana yin sallar a masallatan Delhi.