IQNA

Abdollahian: Iran Na Kokarin Ganin An Ci Gaba Da Tattaunawa Tsakaninta Da Saudiyya

21:24 - March 26, 2022
Lambar Labari: 3487094
Tehran (IQNA) Ministan harkokin wajen kasar Iran, Hossein Amir Abdollahian, ya bayyana cewa kasarsa a shirye ta ke ta shiga zagayen tattaunawa na biyar da Saudiyya.

A wata hira ta musamman da tashar talabijin ta Lebanon Al-Mayadeen, Abdollahian, ya bayyana cewa alakar kasarsa da Saudiyya ba ta da kyau, kuma matsalar ba daga gare mu ne, amma a shirye muke mu shiga zagaye na biyar na tattaunawa da Riyad.

Ya kara da cewa akwai matsaloli da kalubale a alaka tsakanin Iran da Saudiyya, amma muna aiki tukuru domin ganin cewa kofa na bude ko yaushe domin tattaunawa tsakanin kasashen biyu.

Ya ce ‘’tun cen dama ita Saudiyya ce ya katse alaka da Iran, don kuwa Tehran ba ta da matsala da kasashen larabawa, amma wasu halayen Saudiyya marasa kyau kamar zartar da hukuncin kisa kan mutum 81 sun kawo cikas a alakarmu’’.

Da ya tabo batun yakin da Saudiyya ta ke a Yemen, ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya ce ‘’kare kai da ‘yan Yemen ke yi wannan batu ne wanda ya shafe su na kare hurimin kasarsu, amma muna goyan bayan kawo karshen yakin’’.

Sannan a cewarsa ‘’dora alhakin abunda ke faruwa a Yemen ga Iran, ‘’ba gaskia ne ba’’ kuma mun shaidawa Saudiyya cewa batun Yemen batu ne na ‘yan kasar su ya kamata su zamawa kansu abunda suke so.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4044999

captcha