IQNA

Al-houthi: Amurka Ce Ke Yaki Kan Al'ummar Kasar Yemen Ta Hanyar Karnukan Farautarta

21:48 - March 28, 2022
Lambar Labari: 3487099
Tehran (IQNA) Jagoran Ansarullah ta Yemen Abdul-Malik al-Houthi ya kira Amurka, gwamnatin Isra'ila, da Burtaniya a matsayin wadanda suka shirya mamayar Yemen a 2015 wanda Saudi Arabiya take jagoranta.

Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa su ne kasashen da ke aiwatar da wannan hari," in ji Abdul-Malik al-Houthi a wani jawabi d ya yi ta gidan talabijin a jiya Juma'a.

Ya ce tun daga lokacin da aka kaddamar da mamayar Yemen aka fara aikata laifukan yaki a kan al'ummar kasar.

“Kawancen mamaya sun kai hari kan al’ummar Yemen a kowane wuri, sun yi ruwan bama-bamai kan ababen more rayuwa na al'ummar kasar, tare da kokarin cutar da su ta kowace hanya," in ji Houthi.

Tun a watan Maris din shekara ta 2015 ne dai kawancen ya kaddamar da yaki kan kasar Yemen da nufin sake shigar da tsoffin jami'an kasar da ke kawance da Riyadh da Washington da suka tsere a kan mulkin kasar.

Yaman na fuskantar "yakin tattalin arziki mai tsanani," wanda ke neman kwace albarkatun kasar, don haka, yakin yana azabtar da kowane gida a cikin kasar, in ji shi.

Ya ce ya zuwa yanzu Saudiyya da Amurka da Isra'ila da Burtaniya, sun sace dimbin arziki na mai da wasu daga cikin albarkatun da Allah ya huwacer wa Yemen, wanda kuma dama ita ce babbar manufarsu ta kadamar da yakin, bayan kashe dubban fararen hula mata da kananan yara da tsoffi, tare da rusa daruruwan masallatai, da kasuwanni da asibitoci da makarantu, da cibiyoyin hadadar jama'a da suke neman abin da za su rayu.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4045427

captcha