IQNA

Kasashen Musulmi Da Dama Sun Fara Azumin Watan Ramadan A Yau Asabar

15:39 - April 02, 2022
Lambar Labari: 3487114
Tehran IQNA) Yawancin kasashen musulmi da suka hada da Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar, Kuwait, Bahrain, Masar da Falasdinu da sauransu sun sanar da yau Asabar 2 ga Afrilu a matsayin ranar farko ta watan Ramadan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, kotun masarautar Saudiyya, da ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Qatar sun  bayyana Asabar a matsayin ranar farko ga watan Ramadan na shekara ta 1443.

Kasashen Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain da Kuwait da kuma Yemen sun sanar da cewa an tabbatar da ganin jinjirin watan, kuma a sakamakon haka Asabar ce  daya ga watan Ramadan.

Ofishin kula harkokin 'yan Sunna na kasar Iraki da ma'aikatar kula da harkokin yankin Kurdistan da ke arewacin kasar ma sun sanar da Asabar  a matsayin ranar daya ga watan Ramadan a cikin jawabai daban daban.

Ita ma majalisar fikihu ta ma'aikatar da ke kula da harkokin addini  ta kasar Siriya ta jaddada a cikin wata sanarwa cewa Asabar ce daya ga watan Ramadan a kasar.

Shi ma babban Muftin birnin Kudus da yankin Falasdinu Sheikh Mohammed Hussein ya tabbatar da ganin jinjirin watan.

A halin da ake ciki kasashen Jordan da Oman da Iran sun sanar da ranar Asabar a matsayin karshen watan Sha'aban, sannan kuma Lahadi a matsayin ranar farkon watan Ramadan.

Ayatullah Sistani ya ayyana ranar Lahadi a matsayin farkon watan Ramadan a Iraki.

Ofishin Ayatollah Sayyid Ali Sistani a birnin Najaf Ashraf ya ayyana ranar Lahadi a matsayin ranar farko ta watan Ramadan.

Kasashen Singapore, Australia, Brunei, Malaysia da Indonesia suma sun ayyana ranar Lahadi a matsayin ranar farko ta watan Ramadan, kamar yadda shafin yada labarai na Al-Mashhad Al-Yemeni ya ruwaito. 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4046061

 

captcha