IQNA

An ba wa musulmin birnin Minneapolis damar yin kiran sallah da lasifika a cikin watan Ramadan

16:16 - April 05, 2022
Lambar Labari: 3487128
Tehran (IQNA) Mahukuntan birnin Minneapolis sun ce musulmi na iya yin kiran sallah da lasifika a duk shekara a cikin watan Ramadan.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta nakalto Jamal Othman dan majalisar birnin Minneapolis yana fadin cewa masallatai ba za su bukaci neman izinin yin kiran salla da lasifikarsu ba idan aka bi ka'idojin rage hayaniya.

Kafin yanke wannan shawarar, da yawa daga cikin al'ummar musulmin Minneapolis suna yi amfani da kararrawa domin yin ishara da lokacin sallah.

Yusuf Abdullah, babban daraktan kungiyar musulmi ta Arewacin Amurka, ya ce kiran sallah da ke amfani da kalmomi irin su “Allahu Akbar” ma’ana “Allah mai girma ne,” yana ba musulmin da ke kusa da masallacin damar sanin cewa lokacin salla ya yi.

Ya kara da cewa: “Idan ka ji kiran sallah daga gida ko a ofishinka ko kuma a duk inda kake, ka san cewa lokacin salla ya yi, kuma za ka yi shirin.

Abdullah ya ci gaba da cewa: Masu kula da masallatai suna da niyyar ba da hadin kai ga makwabta, don haka ba za a rika yada kiran sallar asuba daga masallatai ba don samun nutsuwa.

Ya jaddada cewa ko ta yaya, wannan sauyi mataki ne na tabbatar da daidaiton addini.

Hukumomin birnin sun yanke shawarar watsa kiran sallah ta lasifika daga karfe 7 na safe zuwa 10 na dare a duk shekara.

Majalisar birnin ta zartas da kuduri da ke bai wa masallatai damar yin kiran sallah sau uku (Azahar, La'asar, Magariba) matukar dai sautin bai wuce wani matsayi ba.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4047011

captcha