IQNA

Shugaban Yemen Mai Murabus Ya Mika Aikinsa Ga Wani Kwamiti

15:49 - April 07, 2022
Lambar Labari: 3487136
Tehran (IQNA) Shugaban Yemen mai gudun hijira Abd Rabbo Mansour Hadi ya sanar da mika ikon da yake da shi ga wani kwamitin shugabancin kasa na musamman

Shugaban Yemen mai gudun hijira a Saudiyya, Abd Rabbo Mansour Hadi ya sanar da mika ikon da yake da shi ga wani kwamitin shugabancin kasa na musamman, da zai yi aiki karkashin jagorancin tsohon ministan cikin gida Rashad Al-Alimi.

A jawabin da ya yi ta talbijin, Mansour Hadi, ya ce yanzu kwamitin mai mambobi takwas ne zai ci gaba da tafiyar da sha'anin siyasa, da sojoji, da kuma tsaron kasa, a wani mataki na kawo karshen zubar da jini a kasar ta Yemen.

Ya kuma sanar da korar mataimakinsa Ali Mohsen al-Ahmar daga mukaminsa.

Tuni Saudiyya ta yi maraba da matakin, tana mai neman sabuwar gwamnati ta tattauna da 'yan Houthi saboda samun dawwamammen zaman lafiya da kawo karshen yakin shekaru bakwai da ya daidaita kasar.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4047405

Kafin hakan dama bangarorin da rikicin na Yemen ya shafa sun sanar da tsagaita wuta na tsawon watanni biyu a wani mataki na karfafawa shirin samar da zaman lafiya a kasar.

 

captcha