Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na iqna cewa, sakamakon bullar cutar corona da kuma matsalolin kiwon lafiya, kasashen ketare ba su halarci taron baje kolin kur’ani na kasa da kasa karo na 29 a wannan shekara kai tsaye ba, kuma rumfar ayyukan kur’ani ta Rumfar Cibiyar Hubbaren Imam Hussain ita ce rumfar da aka kafa a babban dakin baje kolin.
Rukunin ya kunshi bangarori daban-daban inda aka rika baje kolin fastoci na ayyukan cibiyar yada ayyukan alkur'ani ta kasa da kasa da kuma Darul kur'ani, wadanda dukkaninsu ke da alaka da Hubbaren Imam Hussain (AS).
Sayyid Qasim Al-Batat shugaban rumfar ya shaidawa kamfanin dillancin labaran iqna cewa: A bangaren ayyuka na cibiyar yada kur'ani ta kasa da kasa, allunan ayyukan cibiyar sun hada da darussa na horar da malaman kur'ani a kasar Indonesia, da'irar kur'ani a Pakistan, da kuma baje kolin kur'ani na kasa da kasa a Al-Harmain."
Ya kara da cewa wani dutsen marmar da ke cikin harabar hubbaren Husaini da babbar tuta na hubbaren Imam Husaini (AS) na daga cikin ayyukan da aka gabatar a wannan rumfar da kuma gudanar da taron karawa juna sani a wajen rufe taron baje kolin kur'ani na duniya.
https://iqna.ir/fa/news/4050624