IQNA

Darajojin tauhidi; Wane ne ya yi halitta kuma wa ya shiryar?

16:17 - April 20, 2022
Lambar Labari: 3487195
Tehran (IQNA) Allah shi ne kadai mahaliccin talikai kuma yana shiryar da halittu  Amma wasu ba su yarda da wannan shiriyar ba, sai suka zabi wanin Allah a matsayin majibincinsu; Amma wannan zabin kamar zabar makanta ne da tafiya a kan tafarkin duhu.

Alkur'ani mai girma yana cewa: "Ka ce: Wãne ne Ubangijin sammai da ƙasa? » Ka ce: « Allah » . Ka ce: « Ashe fa, kun riƙi waɗansu masõya baicin Shi, waɗanda ba su mallaka wa kansu wani amfãni ba kuma haka bã su tũre wata cũta? » Ka ce: « Shin makãho da mai gani sunã daidaita? Kõ shin duhu da haske sunã daidaita? ko sun sanya ga Allah waɗansu abõkan tãrayya waɗanda suka yi halitta kamar halittarSa sa'an nan halittar ta yi kama da jũna a gare su? » Ka ce: « Allah ne Mai halitta kõme kuma Shĩ ne Maɗaukaki, Marinjãyi» (Raad / 16)

Wannan aya tana daya daga cikin mafi girman ayoyin Alkur'ani na tauhidi. Wannan ayar tana yin tambayoyi ne game da Allah da shiryarwar 'yan Adam a cikin duniyar halitta. A farkon wannan ayar, ya yi tambaya: "Wane ne Ubangijin sammai da ƙasa?"

Maudu’in wannan bangare na ayar ba yarda da Allah ba ne, amma bahasin “Ubangiji” yana nufin tafiyar da al’amuran duniya da Allah yake yi.

Akwai ainihin bambanci a nan. Fir’auna bai ce “Ni ne Allah ba”, amma ya ce “Ni ne Ubangijinku Maɗaukaki” (Naza’at / 24); Wato ya yi iƙirarin cewa shi ne mai mulkin duniya, ba mahaliccin duniya ba.

Alkur'ani yana cewa: " kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã Shi  ba, ( sunã cẽwa ) « Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja." Shi ya sa a kullum muke kiran wadannan mutane mushrikai, saboda sun riki abokan tarayya da Allah.

Amma wadanda suka yarda da cewa Allah shi ne majibincinsu, ba wai a magana kadai ba, har a aikace, halayensu su zama na Ubangiji, kuma ma'auni da tushen motsinsu da maganarsu su kasance a tafarkin Allah kuma ga Allah.

Don haka ne ake yin abin da aka ambata a cikin wannan ayar ta hanyar tambaya don mutum ya zabi tafarkinsa.

 

https://iqna.ir/fa/news/4042844

captcha