IQNA

Martanin duniya game da shirin gwamnatin yahudawa na gina sabbin matsugunnai

22:06 - May 07, 2022
Lambar Labari: 3487262
Tehran (IQNA) A ranar Juma'ar da ta gabata ce sashen tsare-tsare na gwamnatin yahudawan Isra’ila ya sanar da taron kwamitin tsare-tsare na majalisar koli, inda taron ya sanar da amincewa da shirin gina rukunin gidaje 4,000 a cikin yankunan Falastinawa.

Matakin na zuwa ne a lokacin da ake shirye-shiryen ziyarar shugaban Amurka Joe Biden a Isra’ila, kamar dai yadda cibiyar yada labaran gwamnatin Falastinu ta sanar.

Kungiyar hadin kan Larabawa ta yi gargadin kan aiwatar da shirin gwamnatin yahudawan na gina sabbin gidaje 4,000 ga yahudawa ‘yan share wuri zauna, tare da rusa kauyuka 12 na Falastinawa a yankin Yata da ke lardin Hebron.

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, ofishin sakataren kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ya fitar da bayani, wanda a cikinsa ya bayyana shirin na Isra’ila a matsayin babban karfen kafa ga duk wani yunkuri na samar da sulhu tsakanin Isra’ila da Falastinawa.

Kungiyar ta yi gargadin illar da wannan shiri zai haifar dangane da zaman lafiya da tsaro a duniya, inda ta bayyana hakan a matsayin laifi na kabilanci ga al'ummar Palastinu.

Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta bayyana cewa: Wadannan tsare-tsare na nuna irin girman wariyar da ake nuna wa Palasdinawa a kan idanun duniya, wanda kuma yin gum da bakuna da kasashen duniya ke yi kan hakan, shi ne ke karfafa gwiwar Isra’ila wajen ci gaba da yin hakan.

Kungiyar ta jaddada bukatar kasashen duniya musamman kwamitin sulhu da su yi aiki da alhakin da ya rataya a wuyansu da kuma dakatar da gina matsugunan yahudawa a cikin yankunan Falasdinawa da Isra’ila ta mamaye.

 

 

 

4055281

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha