IQNA

22:52 - May 11, 2022
Lambar Labari: 3487279
Tehran (IQNA) A Maroko yau Laraba ne ake bude taron ministoci karo na 9 na kungiyar hadin gwiwa ta duniya kan yaki da kungiyar Daesh ko IS.

Wannan taro, wanda Maroko da Amurka suka shirya, zai ba da "muhimmanci ga nahiyar Afirka", a cewar sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Morocco ta fitar.

Kimanin tawagogi hamsin ne ake sa ran zasu halarci taron na Marakesh, ciki har da 15 daga Afrika.

Wannan shi ne karon farko da ake gudanar da wannan taro a nahiyar.

Daga cikin bakin na Afirka akwai kasashe da suka fito daga yammacin Afirka, kamar Burkina Faso, Jamhuriyar Nijar da Benin.

A shekarar 2014 ne aka kafa kungiyar ta yaki da kungiyar ta IS, wacce ta kunshi malalarta tamanin.

 

4056379

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: