IQNA

Ana Gaba Da Yin Tir Da Isra’ila Kan Kisan ‘Yar Jarida Shireen Abu Akleh

20:08 - May 12, 2022
Lambar Labari: 3487283
Tehran (IQNA) Bangarori daban-daban a duniya na ci gaba da mayar da martani dangane da kisan da Isra’ila ta yi wa fitacciyar ‘yar jarida a Palestine Shireen Abu Akleh a jiya Laraba.

Kungiyar ‘yan jarida ta duniya ta fitar da bayanin yin Allawadai da kakkausar murya kan kisan Shireen, tare da dora alhakin hakan a kan gwamnatin Isra’ila, kamar yadda kungiyar ta bukaci da a gudanar da bincike kan lamarin, wanda zai kunshi bangarori na kasa da kasa.

Su ma a nasu bangaren Amurka da Tarayyar Turai da kuma Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa, da kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, duk sun bukaci da a gudanar da bincike na bangarori masu kansu kan wannan lamari.

A nata bangaren gwamnatin Falastinawa ta bayyana cewa, yanzu haka ta fara hada fayil-fayil kan wannan batu domin mika shi ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, domin shigar da kara a kan Isra’ila, dangane da kisan Shireen Abu Akleh.

Kungiyoyin Hamas, Hizbullah, Jihad Islami, Ansarullah ta Yemen (Alhuthi) da kungiyoyin gwagwarmaya a Iraki, duk sun fitar da bayanai na yin Allawadai da kisan Shireen.

Sojojin yahudawan Isra’ila sun harbe Shireen Abu Akleh ne a safiyar jiya a lokacin da take daukar rahoto a wani samame da sojojin Isra’ila suka kai kan Falastinawa a yankin Jinin da ke gabar yammacin Kogin Jordan a Falastinu.

4056412

 

captcha