IQNA

Isowar ayarin Hajji na farko zuwa Saudiyya bayan shafe shekaru biyu ba a yi ba

19:03 - June 04, 2022
Lambar Labari: 3487380
Tehran (IQNA) A yau ne wasu alhazan kasar Indonesiya suka isa kasar Saudiyya ta filin jirgin saman Madina. Wannan dai shi ne ayari na farko da mahajjata ‘yan kasashen ketare suka fara shigowa kasar bayan shafe shekaru biyu suna hutu sakamakon bullar cutar korona.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a yau (Asabar) ne wasu alhazan kasar Indonesiya suka sauka a filin jirgin saman Madina, kuma za su tashi zuwa Makka a makonni masu zuwa.

Kasar Saudiyya ta sanar a watan da ya gabata cewa za ta bai wa mutane miliyan daya daga ciki da wajen kasar damar gudanar da aikin Hajjin bana a watan Yunin bana, bayan shafe shekaru biyu ba a yi ba. A bara, kimanin mutane 60,000 kuma a shekarar 2020, kasa da 1,000 ‘yan kasa da baki da ke zaune a kasar ne aka ba su izinin zuwa aikin Hajji.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Saudiyya cewa, a yau jirgin farko na aikin hajjin shekarar 2022 daga kasar Indonesia ya isa filin jirgin saman Muhammad bin Abdulaziz da ke birnin Madina. A cewar labarin, mahajjatan kasar Indonesia 358 ne suka isa Madina a yau, inda wasu da dama daga cikin jami'an Saudiyya suka tarbe su.

Wani jami'in ma'aikatar Hajji Mohammad al-Bajawi ya shaidawa kafar yada labarai ta Al-Akhbariya cewa, "A yau mun karbi rukunin farko na mahajjata daga Indonesia kuma za a ci gaba da tashi daga Malaysia da Indiya."

Ya kara da cewa: “A yau mun yi farin ciki da karbar bakon Allah bayan mun yi hutu na tsawon shekaru biyu sakamakon kamuwa da cutar.

A baya ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta sanar da karin karfin karbar maniyyata, inda ta jaddada cewa ‘yan kasa da shekaru 65 ne kawai za su iya shiga aikin Hajjin bana.

Ma’aikatar ta bayyana cewa mahajjata ‘yan kasa da shekaru 65 ne kawai za su iya zuwa aikin Hajji, matukar sun kammala allurar ta hanyar amfani da alluran rigakafin da ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta amince da su.

Kafin barkewar cutar Corona, tafiye-tafiyen Hajji ya kasance babbar hanyar samun kudaden shiga ga Saudiyya, inda ake samun kusan dala biliyan 12 a duk shekara. A shekarar 2019 (Hajjin karshe kafin bullar cutar Corona Virus), kimanin mutane miliyan 2.5 ne suka halarci aikin Hajji.

 

4061979

 

captcha