IQNA

Azhar: Zagin Annabi (SAW) ta'addanci ne na gaske

18:06 - June 06, 2022
Lambar Labari: 3487385
Tehran (IQNA) Al-Azhar a yayin da take yin Allah wadai da cin mutuncin da wasu jami'an Indiya suka yi wa haramin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ta jaddada cewa, irin wannan dabi'a ita ce hakikanin "ta'addanci" da ka iya jefa duniya baki daya cikin rikici da yake-yake.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na “Russia Today” cewa, kungiyar Azhar ta fitar da sanarwar yin Allah wadai da cin mutuncin da kakakin jam’iyya mai mulkin kasar Indiya ya yi wa manzon Allah (SAW).

Cin mutuncin da wasu 'ya'yan jam'iyyar da ke mulkin Indiya suka yi wa haramin Musulunci ya tayar da hankulan al'ummar musulmi a wannan kasa da ma sauran sassan duniya tare da yin zanga-zanga a bainar jama'a.

Al-Azhar ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: "Abin da kakakin jam'iyyar Bharatiya Janata ya fada na nuna rashin sanin tarihi da dabi'un annabawa da manzanni; Domin sun kasance a kololuwa kololuwa na kyawawan halaye, kuma Allah ya kiyaye su daga alfasha da abin da tsarkaka da gaskiya suke qi.

A cewar sanarwar, Al-Azhar ta dauki abin da wannan jahili da rikon sakainar kashi ya fada game da manya-manyan mutane a matsayin wani abin dariya na cewa duk wani kiyayya ga Musulunci da musulmi ana maimaituwa lokaci zuwa lokaci.

A halin da ake ciki, Al-Azhar ta jaddada cewa, irin wannan dabi'a ita ce hakikanin "ta'addanci" da ka iya jefa duniya gaba daya cikin munanan rikice-rikice da yake-yake, don haka dole ne kasashen duniya su dage da kakkausar murya wajen tunkarar hatsarin wadannan masu cin zarafi.

Idan dai ba a manta ba, a yayin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da cin mutuncin wasu ‘yan jam’iyya mai mulkin kasar Indiya guda biyu ga Manzon Allah (SAW), wannan jam’iyyar ta kori daya daga cikin wadannan mutane biyu tare da dakatar da daya daga cikin mambobin har sai an gudanar da bincike.

Jam'iyyar Bharatiya Janatha mai mulki a ranar Lahadin da ta gabata ta dakatar da zama memba na kakakinta Nupur Sharma saboda kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW) tare da bayyana cewa tana mutunta alfarmar dukkan addinai.

Jam'iyyar ta kuma kori shugaban yada labarai na New Delhi Navin Kumar Jindal daga jam'iyyar saboda kalaman batanci ga musulmi .

 

4062180

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Zagin Annabi
captcha