Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta O.I.C Husain Ibrahim Taha ya bayyana jin dadinsa kan matakin ganawa kai tsaye tsakanin shugaban hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Falasdinawa Mahmud Abbas da shugaban bangaren siyasar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas Isma’il Hanihyya karkashin jagorancin shugaban kasar Aljeriya Abdul-Majid Taboune, yana mai bayyana hakan a matsayin matakin da zai kai ga wanzar da sulhu tsakanin bangarorin biyu.
A ranar Talata 5 ga wannan wata na Yuli ne a yayin zaman taron bikin murnar cikan shekaru 60 da samun ‘yancin kan kasar Aljeriya daga turawan mulkin mallakar Faransa; Shugaban kasar Aljeriya Abdul-Majid Taboune ya hada wata ganawa tsakanin shugaba Mahmad Abbas da Isma’il Haniyya, inda masharhanta ke ganin shiga tsakanin kasar ta Aljeriya za ta iya kawo karshen zaman doya da manja da shugabannin biyu suka dauki tsawon shekaru suna yi, duk da halin tsaka mai wuya da suke ciki sakamakon bakar siyasar Yahudawan Sahayoniyya ‘yan mamaya a Falasdinu.