IQNA

Gudanar da taron Ashura na Imam Husaini (AS) a Nijar

15:56 - August 09, 2022
Lambar Labari: 3487661
Mabiya mazhabar Ahlul bait a Jamhuriyar Nijar sun halarci zaman makokin Ashura na Imam Hosseini duk da ruwan sama.

Kamfanin dillancin labaran Iran ya habarta cewa, Mabiya mazhabar Ahlul bait  a Nijar sun gudanar da taron Ashura na Imam Husaini (AS) a Yamai babban birnin kasar, kuma mahalarta taron sun yi alhini tare da bugun kirji a wannan biki.

Tsofaffi da matasa da mata da kananan yara na Najeriya sun yi matukar taka rawa wajen gudanar da tattakin Ashura da zaman makokin Imam Hussain (AS).

Sheik Saleh Ahmad Lazare babban malami ne wanda ya gabatar da jawabi a wajen taron Ashura na Imam  Hosseini a birnin Yamai, inda ya kuma bukaci al'ummar musulmi da su hada kai don yakar gwamnatin sahyoniyawan da take aikata laifuka kan al'ummar Palastinu.

 

4077150

 

 

 

 

 

 

captcha