IQNA

Ofishin Jakadancin Bangladesh ya karrama makarancin kur'ani dan kasar Masar

15:53 - August 21, 2022
Lambar Labari: 3487722
Tehran (IQNA) Jakadan kasar a Masar ya karrama "Osameh El-Baili Faraj" makaranci dan kasar Masar yayin wani biki a ofishin jakadancin Bangladesh dake birnin Alkahira.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Siddi Al-Balad cewa, Osama Al-Baili Faraj wanda ya yi nasarar zama na daya a gasar kur’ani ta kasa da kasa ta ofishin jakadancin Bangladesh da ke birnin Alkahira, ya samu karramawa a lokacin wani biki da “Mohammed Munir-ul-Islam” Jakadan Bangladesh a Alkahira ya jagoranta.

Osama Faraj yana daya daga cikin mazauna birnin "Bila" da ke lardin "Kafr al-Sheikh" na kasar Masar kuma daya ne daga cikin fitattun ma'abota karatu a wannan zamani na kasar kuma yana da murya mai dadin karantawa.

Ya taso a gidan Al-Qur'ani kuma yana dan shekara 11 ya zama mai haddar Al-Qur'ani tare da samun fa'idar kasancewar malaman Al-Qur'ani da shehunai da Sayyidi "Abdul Wahab Jad" baffansa.

Muhammad Seyyed Tantawi, Abdul Fattah Tarouti, Sheikh Qutb al-Tawil, Sheikh "Ahmed Awad Abu Fayuz" na daga cikin malaman wannan makarancin na Masar.

Usama Faraj a tattaunawarsa da Siddi al-Balad ya yi nasiha ga masu haddace mafari da masu sha’awar kur’ani inda ya ce: “Wasu abubuwa suna da matukar muhimmanci a tafarkin haddar Alkur’ani, kuma ya kamata masu haddar su sani. daya daga cikin wadannan abubuwa shi ne karanta littafin Allah da kyau da kiyaye shi gaba daya.

4079569

 

 

captcha