A jiya Talata, a birnin Hyderabad an yi gagarumar da zanga-zangar yin Allah wadai da matakin da aka dauka na bayar da belinsa da sunan ci gaba da bin matakai na bincike, kuma an tilastawa 'yan sanda sanya dokar hana fita bayan wasu masu zanga-zangar suka yi kokarin zuwa gidansa.
Tun da farko dai dan majalisar dokokin kasar Raja Singh, dan jam'iyyar BJP, wanda ya yi fice wajen tsatsauran ra’ayi, ya wallafa wani faifan bidiyo da ya hada da kalaman batanci ga Annabi Muhammad (SAW), lamarin da ya haifar da bacin rai a birnin wanda akasarin mazauna cikinsa musulmi ne, inda daruruwan jama'a suka taru suna neman a kama shi, kuma Nan take ‘yan sandan suka tsare shi.
Ita ma jam'iyyar Bharatiya Janata mai mulkin kasar, wadda mutumin ke wakilarta a majalisa, ta sanar da dakatar da a matsayin mambanta, saboda yunkurin tayar da zaune tsaye da yak eta hanyar cin mutuncin musulmi da addininsu.
Kalaman Singh sun zo ne biyo bayan wani hari da aka kai wa Munwar Farooqi, wani dan wasan barkwanci musulmi wanda masu kishin addinin Hindu suka gallaza masa, tare da yi masa barazana saboda addininsa.