Kamar yadda shafin al-Kafil ya bayyana, an gudanar da wannan gasa ne domin rubuta dukkan kur’ani a rubuce, daga karshe kuma an zabo ma’abuta kididdigar kasar Iraqi guda 10 da za su halarci gasar, kuma kowannen su ya rubuta sassa uku na kur’ani.
Za a aika da wadannan ayyuka zuwa ga majalissar ilimin kur'ani ta hubbaren Abbasi da ke gundumar "Bab Al Khan" ta Karbala.
Ba za a mayar da ayoyin da aka rubuta a wannan gasa ga masu su ba, kuma wanda ya yi nasara na farko za a ba shi dinari miliyan 5 na Iraqi.
Sauran mahalarta taron da ba su yi nasarar zuwa mataki na farko ba, a karshen za su karbi dinari miliyan uku da 500 na Iraqi.