IQNA

Sabbin labarai daga tarukan  Arbaeen na Hosseini;

Hasashen cewa adadin masu ziyarar arbaeen zai kai miliyan 20 a wannan shekara

16:05 - September 12, 2022
Lambar Labari: 3487841
Tehran (IQNA) Gwamnan Karbala ya yi hasashen cewa maziyarta na gida da na waje miliyan 20 ne za su je wannan lardin domin tunawa da Arbaeen Hosseini.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, gwamnan Karbala nasif al-Khatabi ya bayyana a wani taron manema labarai a jiya Lahadi cewa: Ya zuwa yanzu sama da maziyarta  ‘yan kasashen waje miliyan uku da kuma miliyoyin masu ziyara na gida ne suka yi tattaki zuwa birnin na Karbala domin gudanar da tarukan tunawa da ranar  Arbaeen na Imam Hussain (AS).

Da yake bayyana cewa ana ci gaba da zirga-zirgar maziyarta na gida da na waje don shiga Karbala, ya musanta labarin da aka buga na rufe hanyoyin da ke kan hanyar zuwa Karbala yana mai cewa: Ya zuwa yanzu ba mu ga wata rufe hanya a lardin Karbala da kuma zirga-zirgar maziyarta zuwa wannan lardin ba.

Al-Khattabi ya ci gaba da cewa: Muna hasashen cewa birnin Karbala zai karbi maziyarta  na gida da na waje sama da miliyan 20 har zuwa  karshen taron na Arbaeen.

Manjo Janar "Tahsin Al-Khafaji" mai magana da yawun hedikwatar ayyukan hadin gwiwa, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba rundunar za ta fara shirye-shiryen tsaro na musamman na tarukan  Arbaeen, ya kara da cewa: "Rundunar sojin, baya ga shirin tsaro da kewaye; Sun kuma samar da tsaro, da kuma hanyoyi na yanar gizo, tsare-tsare na kiwon lafiya, hidima a sauran bangarori da masu ziyara ke da bukatuwa.

 

4084872

 

 

captcha