IQNA

Shugabannin 'yan adawa a Sudan:

Al'ummar Sudan ba a shirye suke su yi sulhu da makiya yahudawan sahyoniya ba

16:43 - September 27, 2022
Lambar Labari: 3487920
Tehran (IQNA) Shugabannin 'yan adawa a Sudan sun yi Allah wadai tare da jaddada kalaman shugaban majalisar mulkin kasar na cewa alakar da ke tsakanin Khartoum da Tel Aviv a matsayin sulhu, wadannan kalamai ba sa bayyana ra'ayin al'ummar Sudan saboda makiya yahudawan sahyoniya barazana ce ga hadin kan Sudan da kuma tsaron yankin.

A rahoton al-Quds al-Arabi, shugabannin 'yan adawa a Sudan sun yi tir da kalaman Abdul Fattah al-Barhan, babban kwamandan sojojin Sudan kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na wannan kasa, wanda ya kira dangantakar Khartoum tare da gwamnatin yahudawan sahyoniya dangantaka da ta ginu bisa sulhu tare da bayyana muradinsa na kai ziyara a yankunan Falastinawa da Isra’ila ta mamaye.
 
Sediq Tawar tsohon mamba a majalisar mulkin kasar Sudan ya kira kalaman Al-Barhan da cewa yana bayyana matsayinsa na kashin kansa ga gwamnatin sahyoniyawan yana mai cewa: Wadannan kalamai ba sa wakiltar muradun al'ummar Sudan.
 
Ya kara da cewa: kalaman kwamandan sojojin sun bayyana matsayin wanda ya yi yunkurin juyin mulki ba bisa ka'ida ba kuma ya samo asali ne daga burinsa na kashin kai.
 
Game da lamarin Isra'ila, yana aiki ne bisa ga son ransa ba tare da yin magana ga bangaren gudanarwa ba, kuma tun lokacin da ya yi ganawarsa ta farko da Benjamin Netanyahu, tsohon Firayim Minista na Isra'ila a ranar 3 ga Fabrairu, 2020 ba da sunan al’ummar Sudan ya yi hakan ba.
 
Wannan jagoran 'yan adawar Sudan ya ce: Al-Barhan yana son samun goyon bayan diflomasiyya na Isra'ila da wadannan kalamai domin tabbatar da kasancewarsa a cikin gwamnati, kuma ya yi watsi da hujjojin tarihi da ke jaddada cewa Isra'ila ba ta da alaka ta sulhu da kasashen duniya.

4088099

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Al-Barhan ، kalaman ، sulhu ، makiya ، adawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha