Ahmad bn Tulun, gwamnan Abbasiyawa na Masar daga 868 zuwa 884 miladiyya shi ne ya bada umarnin gina masallacin, kuma an fara aikin a shekara ta 876 miladiyya.
An gina shi a kusa da wani fili mai fadi, masallacin yana da tsohon salon gine-gine na Masar.