IQNA

Dare Na Biyu Na Gasar Karatun Al-Qur'ani Mai Girma A Malaysia

Tehran (IQNA) Masu karatun kur’ani daga kasashe da dama sun gudanar da karatun kur’ani mai tsarki a dare na biyu na gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa ta Malaysia karo na 62.

Taron wanda aka fi sani da Majalisar Karatu da haddar Al-Qur'ani ta kasa da kasa Malaysia, an fara shi a hukumance a daren Laraba a babban birnin Kuala Lumpur fadar mulkin kasar.