Tehran (IQNA) An nuna faifan bidiyo na karatun ''Abdul Rahman Faraj'' dan kasar Masar wanda ya yi nasara a gasar kur'ani ta kasa da kasa ta Rasha karo na 20 a yanar gizo.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Abdulrahman Faraj limamin masallacin Sultan Hassan na kasar Masar ne, wanda ya samu matsayi na biyu a gasar kur’ani mai tsarki ta kasar Rasha karo na 20 da aka gudanar kwanan nan a wannan kasa.
Har ila yau, Limamin Turkiyya Ahmed Kozo ne ya zo na daya sannan Seyed Mustafa Hosseini daga Iran ya zo na uku.