IQNA

Cikar Shekaru Bakwai Da Kisan Gillar Zaria, Najeriya

15:54 - December 13, 2022
Lambar Labari: 3488329
Tehran (IQNA) A jiya ne aka cika shekaru bakawai da kisan gillar da sojoji suka yi a Zaria da ke arewacin Najeriya kan magoay bayan harka Islamiyya karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky.

A ranar A jiya 12 ga watan Disamba ne aka cika shekaru bakawai da kisan gillar da sojoji suka yi a Zaria da ke arewacin Najeriya kan magoay bayan harka Islamiyya karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Kisan gillar ya auku ne a tashin farko daga cibiyar tarukan addini ta Husainiyar Baqiyatollah a garin an Zaria, bayan da sojojin suka zargi magoya bayan Harka Islamiyya da tare wa babban hafan hafsosjin soji na kasar Tukur Burtai hanya, inda suka ce sun bi ta hanyar lalama domin ganin an bude masa hanya, amma magoya bayan Harka Islamiyya suka ki yin hakan.

yayin da ana su bangaren magoya bayan Harka Islamiyya suka bayyana cewa suna gudanar da shirin kafa tutar shigar watan rabiul Awwal domin fara tarukan Maulidin manzon Allah.

Duk da cewa dai sojojin ba su yi bayani kan abin da suka aikata ba bayan kin budewa Burtai hanya, amma dai shedun gadi da ido da kuma hotunan bidiyo da aka dauka daga kusurwoyi daba a lokacin faruwar lamarin, sun tabbatar da cewa sojojin sun bude wutar bindiga na kan mai uwa da wabi, tare da kashe wani adadi na mutane a wurin, akasarinsu magoya bayan harka Islamiyya ne.

Bayan nan kuma sojojin sun kai farmaki kan gidan jagoran harka Islamiyya da ke unguwar Gyalle su, inda a can ma suka kashe mutane masu yawa, kamar yadda shedun gani da ido da kuma wadanda abin ya rutsa da su suka tabbatar, bugu da kari kuma wasu daga cikin hotunan bidiyo da aka dauka da suke nuna wani bangare na abin da ya faru.

Haka nan kuam bayan kisan mutane masu yawa da jikkata wasu, sojojin sun kama sheikh Ibrahim Zakzaky tare da maidakinsa Zinat Ibrahim, kamar yadda kuma daga cikin mutanen da aka kashe a wurin har da ‘yay’yansu guda uku, da kuma kanwarsa gami da dan yayansa.

زکزاکی

Bisa kididdigar da hukumomin jihar Kaduna suka bayar, an bizne gawawwakin magoya bayan harka Islamiyya kimanin 347 a wani fafakeken ramie  a unguwar Mando da ke Kaduna, amma majiyoyin Harka Islamiyya sun sun bayyana cewa adadin mutanen da aka kashe sun fi dubu daya.

Bayan tsare Sheikh Zakzaky na tsawon kusan shekaru shida, daga karshe dai kotu ta sallame bayan kasa tabbatar da dalilai daga bangaren gwamnati kan tuhumce-tuhumcen da aka yi kansa.

Yanzu haka dai akwai cikakkun bayanai a  hannun kotun hukunta  manyan laifuka ta duniya kana bin day a faru a Zaria, bayan da jami’an kotun suka ziyarci Najeriya kuma suka ji tab akin mutane da dama da suka ganewa idannsu abin da ya faru, da kuma dangin wadanda abin ya rutsa da su, tare da karbar kwafi-kwafi na hotuna da kuam hotunan bidiyo na abin da ya faru.

Wannan shi ne karo na bakwai da magoya bayan Harka Islamiyya karkashin jagorancin Shikh Zakzaky suke gudanar da tarukan tunawa da kisan gillar na Zaria.

 

4106602/

 

 

captcha