Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Baladi cewa, an gudanar da wannan gagarumin biki ne a filin wasa na Lansana Conte, inda aka karrama mahardatan kur’ani mai tsarki 190, 23 daga cikinsu mata ne.
Matan da suka haddace kur'ani a wannan bikin sun fito ne daga cibiyoyin Darul-Salam, Othman bin Affan da kuma Noor al-Qur'an. An gudanar da bikin ne karkashin jagorancin Dansa Khroma, shugaban majalisar rikon kwarya ta kasa, da dimbin jami'an gwamnati, jami'an diflomasiyya na kasashen waje da kuma dimbin 'yan kasar.