IQNA

Martanin masu tsatsauran ra’ayi a Faransa kan nuna wata tattala da ta kunshi mata masu lullubi

14:36 - January 26, 2023
Lambar Labari: 3488563
Tehran (IQNA) Matakin da wata kungiya ta Turai ta dauka na nuna  wata talla ta hanyar amfani da hoton mata masu lullubi ya haifar da martani mai zafi daga masu tsatsauran ra’ayi a Faransa.

Gigidan talabijin na Aljazeera ya bayar da rahoton cewa, matakin da hukumar kare hakkin tsarin mulkin Tarayyar Turai ta dauka na buga wata tallar da aka nuna hoton wasu mata da suka hada da mata masu lullubi, ya fusata masu rajin kare akidar ‘yan mazan jiya a Faransa.

David Reeve, wani fitaccen dan kungiyar Recapture France, ya yi tsokaci kan hoton a shafinsa na Twitter, yana mai cewa hijabi ya zama tallar dindindin.

Florence Bergaud Blackler, wata mai fafutuka ta hannun dama ta Faransa, ita ma ta rubuta a shafinta na Twitter cewa: "An yi farin ciki a lullube." A nan hoton hijabi yana da nasaba da gaskiya da kuma kyautatawa.

Ya kara da cewa: Ko shakka babu kungiyar kare hakkin tsarin mulkin Tarayyar Turai na son sake jaddada 'yancin sanya hijabi a Turai.

Wannan ra'ayi na kungiyoyin dama ya haifar da martani da dama, kuma masu suka suna ganin cewa sanya hijabi ko rashin sa wani lamari ne na mutum.

 

4117322

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: martani ، tsatsauran ra’ayi ، nasaba ، mazan jiya ، rubuta ، lullubi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha