IQNA

Rufe Bukin Fasahohi na Alqur'ani a Malaysia

PUTRAJAYA (IQNA) - An gudanar da bikin rufe taron bikin fasahohin  kur'ani na Restu Global Arts a birnin Putrajaya na kasar Malaysia a yammacin jiya Litinin.

Gidauniyar Restu da abokan huldar kasashen waje da suka hada da cibiyar raya al'adu ta Iran da ke Malaysia da taimakon kungiyar al'adu da alaka ta Musulunci (ICRO) ne suka shirya bikin na kwanaki goma.

Ya ba wa baƙi damar halartar nune-nune na musamman, da yin hulɗa da kur'ani da fasaha na Islama da ƴan kasuwa na samfuran Musulunci tare da ƙoƙarin inganta kimar Musulunci a matsayin addini mai haɗaka da lumana.