IQNA

Share Kurar Masallacin Jamkaran kafin Bukukuwan Nisf -Sha’aban

QOM (IQNA) – Ma’aikata sun tsaftace masallacin Jamkaran domin shirya shi domin gudanar da bukukuwan tsakiyar watan Sha’aban.

Nisf sha’aban, ko kuma ranar 15 ga watan Sha’aban, ita ce ranar da aka haifi Imami na goma sha biyu, Imam Zaman (Allah ya gaggauta bayyanar da shi).

A duk shekara a wannan rana mai albarka, dubban daruruwan masallata ne ke ziyartar masallacin Jamkaran.

Ranar 15 ga watan Sha’aban za ta kama ne a ranar Laraba 8 ga watan Maris na wannan shekara.