Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Araby Al-Jadeed cewa, babban sakataren MDD Antonio Guterres a cikin wani sako na ranar yaki da kyamar musulmi ta duniya, ya yi kira da a dauki matakin kawo karshen kyamar musulmi.
Babban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada a cikin wannan sakon cewa: kusan Musulmai biliyan biyu ne ke rayuwa a wannan duniyar tamu kuma suna nuni ne ga bil'adama tare da bambancin ban mamaki. Sai dai a lokuta da dama ana yi masu son zuciya ba tare da wani dalili ba sai al’amuran mazhaba.
Yayin da yake ishara da cewa nuna wariya ga mata musulmi saboda jinsi da launin fata da kuma imani na daya daga cikin mafi munin sakamakon kyamar addinin Islama, Guterres ya bayyana cewa: Wannan kiyayya da ke kara ta'azzara wani bangare ne na sake farfado da kishin kabilanci, akidun wariyar launin fata na Nazi da kuma cin zarafin jama'a. sun hada da Musulmai da wasu tsirarun Kiristoci.
A wani bangare na sakon nasa, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a yi yaki da bangaranci da kiyayya da ke kara yaduwa a sararin samaniyar intanet.
Antonio Guterres ya kuma jaddada ta hanyar karanta ayar kur’ani mai tsarki cewa sako da manufar Musulunci da ya zo wa mutane shekaru 1400 da suka gabata shi ne zaman lafiya da soyayya da kuma gafara.
Don yin bayanin nasa, Guterres ya karanta ma’anar Turanci ta aya ta 6 a cikin suratu Taubah: (Kuma idan daya daga cikin mushirikai ya fake da kai (ya koyi addini), to, ka ba shi mafaka, ya ji kalmar Allah.
A cikin wadannan za a iya ganin bidiyon wannan jawabi na Alkur'ani: