An gudanar da taron daren lailatuk kadari (dare na 23 ga watan Ramadan) tare da karatun adduar Joshan Kabir tare da halartar dimbin maziyarta a hubbaren Imam Hussain (a.s) da kuma tsakanin wuraren ibada guda biyu.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, miliyoyin maziyarta daga kasashen Iraqi da larabawa da kuma na musulmi ne suka gudanar da tarukan daren lailatul qadr a daren na uku ta hanyar gabatar da addu’o’i da karatun kur’ani mai tsarki da addu’o’i a kusa da haramin Imam Hussain (a.s.) da Sayyidina Abul Fazl al-Abbas (a.s.).
Wannan taro ya gudana a daren Juma'a cikin yanayi mara misaltuwa, kuma masoya Ahlul Baiti (AS) sun bayyana shaukinsu da kuma gabatar da bukatarsu ga Allah.