IQNA

An wulakanta kur'ani a Denmark a karo na hudu a cikin wata 1 da ya gabata

16:44 - April 29, 2023
Lambar Labari: 3489060
Tehran (IQNA) Wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta yi wa kur'ani mai tsarki zagi a karo na hudu a cikin wata guda a wani danyen aikin da suka aikata a gaban ofishin jakadancin Turkiyya da ke birnin Copenhagen na kasar Denmark.

A rahoton  Anatoly, wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta sake kai hari kan kur'ani mai tsarki a gaban ofishin jakadancin Ankara da ke Copenhagen, babban birnin kasar Denmark a jiya, Juma'a 28 ga watan Afirilu.

Wani dan kungiyar masu tsattsauran ra'ayin kishin kasa da kyamar Musulunci mai suna "Patriot Live" ne ya kai wannan hari a gaban ofishin jakadancin Turkiyya.

Wanda ya kai wannan hari na tunzura jama’a ta hanyar daga tutoci masu nuna kyama da rera taken cin mutuncin addinin Musulunci, ya yada lokacin da ake kai wa Kur’ani mai girma da tutar Turkiyya hari kai tsaye a shafinsa na Twitter.

Wakilin kamfanin dillancin labaran Anatolia ya sanar da cewa, bakin haure Turkiyya da suka je ofishin jakadancin kasarsu domin kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki, sun bayyana rashin gamsuwarsu da wulakanta kur'ani mai tsarki tare da yin Allah wadai da shi.

Ya ce lokacin da daya daga cikin Turkawa ya daga tutar kasarsa daga kasa, 'yan sandan Denmark sun shiga tsakani tare da gargadi maharin.

Rundunar ‘yan sandan kasar Denmark ta gargadi ‘yan kasar Turkiyya da ke kusa da ofishin jakadancin kasarsu da ke birnin Copenhagen da kada su shiga tsakani don nuna adawa da wannan aika-aika da kuma ci gaba da daukar matakan tsaro don kare wanda ya aikata wannan aika-aika.

 

 

4137114

 

 

captcha