Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada labaran Falasdinu Ben Ghafir, wanda ya shiga masallacin Al-Aqsa bisa tsauraran matakan tsaro, ya gudanar da ayyukan ibada da koyarwar Talmud a yankin gabashin wannan masallaci.
Tun da sanyin safiyar yau ne Bin Ghafir ya isa gaban katangar Baraq da ke kusa da masallacin Al-Aqsa bisa tsauraran matakan tsaro.
Gidan rediyon yahudanci na "Kan" ya sanar da cewa a lokacin kutsa kai cikin Masallacin Al-Aqsa, Ben Ghafir ya yi ikirarin cewa barazanar Hamas ba ta da wani amfani kuma mu ne ma'abota Kudus da wannan kasa!
Wannan harin da ministan haramtacciyar kasar Isra'ila ya kai kan masallacin Al-Aqsa ya haifar da cece-ku-ce, kuma tun da safiyar yau sama da 300 'yan sahayoniyawan mamaya suka kai hari kan masallacin Al-Aqsa.
Hamas: Ba za mu bar Masallacin Al-Aqsa kadai ba
Kakakin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a birnin Kudus ya jaddada cewa ba za mu taba barin masallacin Al-Aqsa shi kadai ba, kuma alhakin dukkanin sakamakon mummunan harin da ministocin haramtacciyar kasar Isra'ila da 'yan mamaya na yahudawa suke yi yana kan gwamnatin sahyoniyawan ne.