Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Al-Safir ya bayar da rahoton cewa, wata likitar kasar Faransa mai suna Evelyn Geneviève ta yanke shawarar karbar addinin musulunci bayan ta zauna da musulma na tsawon lokaci a birnin Al-Nazour da ke arewacin kasar Morocco.
Wannan Likitan yar kasar Faransa ta sanar da Musulunta ne ta hanyar bayyana a hedkwatar karamar hukumar kimiyya ta yankin Al-Nazour da kuma halartar gungun 'yan majalisar da malamai.
Wannan mace Bafaranshiya, likita ce da ta kware a fannin tabin hankali da take aiki a Al-Nazour, tana zaune a wannan birni tare da mijinta tsawon shekaru.
A wannan karon majalisar kimiya ta Al-Nazour ta gabatar da kwafin kur'ani mai tsarki guda biyu ga wannan sabuwar musulunta da mijinta.