Ma’aikata Suna dinka kyallen da allura na musamman sannan su dinka farar rigar lilin a dukkan bangarori hudu na dakin Ka'aba, domin gudanar da aikin Hajji, inda miliyoyin alhazai daga kasashe daban-daban suke ziyartar wannan wuri mai albarka domin sauke farali.