Karatun Mahmoud Shahat Anwar a otel "Hilton" da ke kasar Saudiyya
An yada wani bidiyo da fitaccen makaranci na Masar Mahmoud Shahat Anwar ya yi karatun kur’ani a otal din Hilton da ke Riyadh babban birnin kasar Saudiyya a yanar gizo.
Mahmoud Shahat Anwar, wanda ya tafi kasar Saudiyya ba da dadewa ba, ya halarci wani taron karatun kur’ani a otal din Riyadh Hilton inda ya karanta ayoyin Suratul Shams a wannan otal.