Dubban daruruwan alhazai ne daga sassa daban-daban na duniya suka isa babban masallacin Harami na Makkah domin gudanar da Tawafin Qudum (Tawaf na isowa) yayin da aka fara gudanar da aikin hajji mafi girma na shekara shekara cikin shekaru da dama a birnin mai alfarma.