IQNA

Makabartar Jannat Al-Mu'alla a Makka a cikin hotuna

MAKKA (IQNA) – Jannat al-Mu’alla makabarta ce a birnin Makka na kasar Saudiyya, inda aka binne da yawa daga cikin ‘yan uwa da kakannin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da suka hada da Sayyida Khadija, Abdul Mudallib, da Abu Talib (amincin Allah ya tabbata a gare su).

Sarkin Saudiyya Ibn Saud ya rusa wannan makabarta a shekarar 1925, duk da nuna kin amincewa da kuma yin tir da Allawadai da  al'ummar musulmin duniya suka yi kan hakan.