KARBALA (IQNA) – Dubban Daruruwan jama’a ne suka taru a hubbaren Imam Husaini (AS) da kuma Sayyid Abbas (AS) da ke Karbala domin tunawa da ranar Ashura a ranar 29 ga Yuli, 2023.
Ranar Ashura ita ce rana ta 10 ga watan Muharram, kuma rana ce ta juyayin shahadar Imam Husaini da sahabbansa a wakiar Karbala a shekara ta 680 miladiyya.