IQNA

Paparoma: Tozarta Al-Qur'ani wani cikas ne ga tattaunawa tsakanin addinai

15:58 - August 03, 2023
Lambar Labari: 3489583
Dangane da wasikar da wani muballig musulmi dan kasar Argentina ya rubuta wa Fafaroma Francis da a dauki kona kur’ani a kasashen Sweden da Denmark a matsayin aikin dabbanci da kuma kawo cikas ga tattaunawa tsakanin addinai.

Paparoma: Tozarta Al-Qur'ani wani cikas ne ga tattaunawa tsakanin addinai

A rahoton Al-Mayadeen, shugaban mabiya darikar katolika a duniya ya rubuta amsar wasikar Hojjatul-Islam Abdul Karim Paz wakilin addinai a cibiyar muslunci ta kasar Argentina (FIAS) ya bayyana kona kur’ani da aka yi a matsayin cikas ga tattaunawar addinai da zamantakewar ɗan adam kuma aikin dabbanci.

Fafaroma Francis ya rubuta a martani ga wannan malamin mazhabar ahlul bait:

“Dr. Abdul Karim Baz, ya dan uwana, na gode kwarai da wannan wasiƙar da ka rubuta.

Labarin kona Al-Qur'ani abu ne mai matukar muni. Wadannan ayyuka suna cutar da kuma hana tattaunawa ta mutuntaka  tsakanin mutane.

yayanku francis"

 

A makon da ya gabata ne Abdulkarim Paz ya rubuta wasika zuwa ga Paparoma Francis, shugaban darikar Katolika, inda ya soki yadda ake yawaita kona kwafin kur'ani na musulmi da cewa yana cutar da hadin kan mabiya addinan Ibrahim.

Watanni biyu da suka gabata Paparoma yayi Allah wadai da kona kur'ani a kasar Sweden. Ya ce a wancan lokacin: Ina fushi da kyama da wadannan ayyuka. A wata hira da jaridar Al-Ittihad ta Hadaddiyar Daular Larabawa, ya bukaci jama’a da su amince da ka’idojin da aka ambata a cikin takardar ‘yan uwantakar ‘yan Adam.

Paparoma ya ce: "Duk wani littafi da aka dauke shi da tsarki dole ne wadanda suka yi imani da shi su girmama shi." Bai kamata a yi amfani da 'yancin faɗar albarkacin baki a matsayin uzuri don wulakanta wasu ba.

Yawan wulakanta kur'ani mai tsarki da aka yi a kasashen Sweden da Denmark a cikin watanni biyu da suka gabata ya haifar da fushin musulmi a duniya. Da yawa daga cikin musulmi masu fafutuka na son daukar matsaya daya a kan kasashen da ke ba da lasisin tozarta kur'ani. Wasu masana sun gabatar da saka takunkumin tattalin arziki da yanke huldar diflomasiyya da kasashen musulmi za su iya yi a matsayin daya daga cikin hanyoyin da za a bi wajen hana maimaita wulakanta wurare masu tsarki na Musulunci.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4159923

 

captcha