IQNA

Ana samun karuwar laifuffuka bisa kyamar Musulunci a Jamus

19:18 - August 16, 2023
Lambar Labari: 3489655
Yawan kyamar addinin Islama a Jamus ya haifar da damuwa game da makomar gaba.

A bisa rahoton Ellawa, a farkon rabin shekarar 2023, hukumomin Jamus sun rubuta laifuka sama da 250 da suka shafi kyamar Musulunci. Bisa kididdigar da aka yi, an yi rajistar laifuffuka 258 kan musulmi da masallatai har zuwa watan Yuni, wanda 134 suka kasance a rubu'i na biyu na wannan shekara.

Wadannan bayanai na nuni da karuwar hare-haren wuce gona da iri kan musulmi da matsugunansu a kasar Jamus idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, inda aka yi rajistar irin wadannan laifuffuka 100 a farkon rabin shekarar, kuma mutane 17 suka jikkata, akasari daga hannun masu tsattsauran ra'ayi.

Sai dai kuma, rabin na biyu na shekarar 2022 an samu karuwar yawan laifukan da ake aikatawa, lamarin da ke kara nuna fargabar karuwar laifukan wariyar launin fata a bana.

Petra Pau, mamba a majalisar dokoki game da haka ta bayyana cewa: Idan aka yi la'akari da ayyukan tunzura 'yan rajin kare hakkin bil'adama da kuma yadda ake kara daidaita taken kyamar Musulunci, abin takaici ba abin mamaki ba ne yadda masu fafutuka ke ganin sahihancin ayyukansu.

Ya kara da cewa: Tattaunawar wariyar launin fata a kan wannan lamari ya haifar da yanayi na gaba da rashin hakuri.

Wannan dan majalisar ya bayyana cewa: Mutanen da suke bayyana kansu a matsayin musulmi suna kara fuskantar barazana. Wannan lamarin bai kamata ya ci gaba da haka ba.

Bisa kididdigar da hukumar binciken manyan laifuka ta Jamus ta fitar kimanin watanni biyu da suka gabata, a shekarar 2022 an samu fiye da 610 na laifukan da suka shafi musulmi, ciki har da harin da aka kai a wani masallaci a birnin Hanover da kuma kona kantuna.

 

 

 

4162781

 

 

captcha