IQNA

Babban Masallacin Qom, daya daga cikin tsofaffin masallatai a Iran

Qom (IQNA) Masallacin Qom mai fadin murabba'in mita 6000 an gina shi ne a karni na uku na hijira kuma yana daya daga cikin tsofaffin masallatai a Iran.

Duk da cewa ba a yi amfani da ƙarfe ba wajen gina wannan katafaren masallaci da kurbarsa, amma har yanzu yana da ƙarfi bayan ƙarnoni.