Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ayatullah Sayyid Ali Sistani shugaban mabiya mazhabar Ahlul bait a kasar Iraki ya bukaci mutane da su guji wuce gona da iri kan Ahlul Baiti (AS).
Ya sanar da wannan bukatar ne a matsayin martani ga wata tambaya da aka yi kan wasu lamurra da suka shafi Imam Ali (a.s.) da Imam Husaini (a.s.)
Ayatullah Sistani ya sha rokon masu magana da mawaka da masu yabon Ahlul Baiti (A.S) da su guji wuce gona da iri a harkokin addini.