Harin dai ya haifar da rashin tsaro a yankunan da yahudawa suka mamaye. A halin da ake ciki dai sojojin na haramtacciyar kasar Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare ta sama a zirin Gaza lamarin da ya yi sanadiyar lalata wuraren zama da masallatai tare da lakume rayukan daruruwan mutane. fararen hula.